Matthew 11

Yesu da Yohanna Mai Baftisma

1Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yǎ koyar yǎ kuma yi waʼazi a garuruwan Galili.
Da Helenanci a cikin garuruwansu


2Saʼad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa 3su tambayi shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?”

4Yesu ya amsa, ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani: 5Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana ta da matattu, ana kuma yi wa matalauta waʼazin labari mai daɗi. 6Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.”

7Saʼad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna: “Me kuka je ƙallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne? 8In ba haka ba, to, me kuka je ƙallo? Mutum mai sanye da riguna masu kyau ne? Aʼa, masu sa riguna masu kyau, ai, a fadan sarakuna suke. 9To, me kuka je ƙallo ne? Annabi? I, ina gaya muku, ya ma fi annabi. 10Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa:

“ ‘Zan aiki ɗan saƙona yǎ sha gabanka,
wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’
Mal 3.1

11Gaskiya nake gaya muku: A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma. 12Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yǎ zuwa yanzu, mulkin sama yana sha da ƙyar, fitanannu kuma sun kama mulkin sama sun riƙe gam. 13Gama dukan Annabawa da kuma Doka sun yi ta annabci har yǎ zuwa kan Yohanna. 14In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Eliya da dā ma zai zo. 15Duk mai kunnen ji, yǎ ji.

16“Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa:

17“ ‘Mun yi muku busa,
ba ku kuwa yi rawa ba,
mun rera waƙar makoki,
ba ku kuwa yi makoki ba.’
18Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’ 19Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da “masu zunubi.” ’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”

Kaiton Biranen da ba Su Tuba Ba

20Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba. 21“Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka. 22Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shariʼa, fiye da ku. 23Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? Aʼa, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yǎ zuwa yau. 24Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shariʼa.”

Hutu domin Waɗanda Suka Gaji

25A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara. 26I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi.

27“Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yǎ bayyana musu shi.

28“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu. 29Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawaliʼu ne marar girmankai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. 30Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”

Copyright information for HauSRK